Wadanda Suka Sace Tagwaye A Zamfara Sun Yi Nadama

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Biyo bayan kame gungun yan fashin nan a Zamfara da suka sace yan biyun nan a kauyen DAURAN dake karamar Hukumar Zurmi, muryar Amurka ta tattauna da daya daga cikin jagororin yan Bindigar.

Daya daga cikin ‘yan fashin, Nafiu Usman Wanda Yaro ne dan shekara 28, dan asalin karamar hukumar Zurmi ya ce sun yi Sabo ne da yan bindigar yayin da Suke zuwa sayayya a kauyukansu.

Talla

Ya ce ta haka suka Samu sukai Sabo dasu a hankali a hankali har Suke Jan hankalinsu suma Suke zama yan bindigar.

Yace wani Mai suna Yellow shi ya basu shawarar sace yan Matan Ana dab da yin bikinsu, Nafiu yace sun yi amfani da babura shida  suka je har gida suka sato Tagwayen.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Nafiu  ya zargi yan’uwansa yan bindigar da suka shirya karban kudin fansar da yi masu magudi, inda yace bayan sun karbo Naira miliyan goma sha biyar, sai suka masu karyar cewa Naira Milyan Goma ne, inda suka raba Naira dubu Dari biyar biyar, a hakan ma wasu nasu bai zo hanun su ba.

Daga nan yayi nadamar yadda suka Rungumi wannan sana’ar ta satar mutane.

A nasa bayanin, Kakakin rundunar yansanda Najeriya Moshood jimoh ya ce kimanin manya manyan bindigogi Guda shida, harsasai da takubba suka kama a hanun yan bindigar.

Dukkannin yan bindigar dai zamfarawa ne, Kuma ko a baya Wamban jihar Abdul’Azeez Yari Abubakar Ya koka da Cewar yan bindigar dake aiwatar da kashe kashe dukksnninsu yan jihar ne.

 

 

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: