KannywoodTarihi

Wace Ce Jaruma Fati Muhammad?

An haife ta 15 ga watan Yuni 1982, tana da kusan shekara 39 Kenan a yanzu.
Fati Muhammad wacce wasu kewa lakabi da beni ba ka tsufa, yar asalin wanan jiha ce ta Kano. An haifeta a unguwar Rijiyar Lemo inda ta fara karatunta na primary a Tukuntawa Special Primary school.

Hajiya Fati dai ta yi karatunta na gaba da sakandare a London, Pittsburg Regional College tsakanin shekarar 2000 zuwa 2005.

Ita dai hajiya Fatima ta taba aure inda ta auri Sani Musa Mai Iska wanda shi ma jarumi ne a masana’antar kannywood, amma auren ya mutu bayan shekaru biyar da daura shi.

Ita ce yar auta a gidansu daga cikin su hudu.
Hajiya Fati dai, Allah bai bata haihuwa ba lokacin auren.

Ta ce: tana fatan wani auren nan gaba kadan kuma tana fata ba da dadewa ba.

Fati dai ta yi fim sama da 200, a ciki akwai, Hallaci, Sangaya, Mujadala, Al-Mustapha, Tawakali, Aljannar Mace, Gasa, Tutar So, Abadan Da’iman, Dan Baiwa, Mugun Nufi, Kuduri, Farari, Zarge, Nau’in So dss.

Allah kara lafiya da basira Hajiya Fatima Muhammad

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: