Wasanni

Wa zai maye gurbin Neymar?

Tun bayan da dan wasan Brazil Neymar ya ce zai bar Barcelona, ake ta rade-radi da hasashen wanda zai mare gurbinsa.

Wasu dai na ganin Barca za ta yi kokarin sayen takwaransa na Brazil kuma dan Liverpool Philippe Coutinho.

Tuni dai dama aka ce suna nemansa tun kafin Neymar ya ce zai bar kungiyar.

Sai dai ganin makudan kudin da za su karba kan Neymar, babu shakka duk dan wasan da za su nema, to sai aljihunsu ya yi kuka.