Daga karshe waɗanda suke suka ta kan rufe boda sun dawo suna yaba man da suka ga alfanun abin – Inji shugaban kasa Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ƴan Najeriya da suka rika sukarsa saboda rufe iyakokin kasar na kasa daga karshe sun dawo suna yaba masa a kai.
Ya ce ya dauki matakin rufe iyakokin ne domin karfafa wa ƴan Najeriya gwiwa kan samar da abincin da suke bukata.
Shugaban mai barin-gado ya bayyana hakan ne a yau Talata lokacin da yake kaddamar da sabon ginin hedikwatar hukumar hana fasa-kwauri wato kwastan a gundumar Maitama da ke babban birnin tarayyar kasar, Abuja.
Ya ce yana sane ya bayar da umarnin rufe iyakokin saboda ya san ƴan Najeriya suna sayo shinkafa daga waje su ba Nijar da wasu kasashe sannan su shigo da sauran kasar.
Shugaban ya ce da arzikin da Najeriya take da shi tana da mutane da kasa da kuma yanayi, arzikin da kasashe ‘yan kadan ne a duniya suke da shi.
Sai dai ya ce idan aka duba za a ga cewa daga tafkin Chadi zuwa Jamhuriyar Benin akwai nisan sama da kilomita 1,600 saboda haka Allah ne kadai zai iya tsare wannan iyaka da kyau.
”Saboda haka kana bukatar mutumin da yake da karfi da kwarewa ya sa ido a kan wanna aiki,” in ji Buharin.
Shugaban ya ce ya rufe iyakar ne mai tsawon kilomita 1,600 domin ‘yan Najeriya su rika noma abincin da suke bukata, idan kuma ba haka ba sai dai mutum ya mutu.
Ya ce abin da ya sa ya dauki wannan mataki ke nan wanda kuma daga baya an kasar suke yabawa a kai.
Add Comment