Video: Kada Wanda Ya Kara Cina Gyaran Turanci – Inji Adam A Zango

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Fitaccen jarumin wasan kwaikwayon Hausa na Kannywood kuma mawaki Adam Abdullahi Zango ya gargadi mabiyansa a shafukan sada zumunta da su daina cinsa gyara a yayin da furta ko ya rubuta wani bayani na tutanci.

Jarumin yayi wannan gargadi ta wani hoton bidiyo da ya dora a shafinsa na sadarwar zamani ta instagram. Jarumin ya bayyana cewar bai taba cema wani yayi makaranta ba, illa iyaka duk turancin da yake kokarin yi to tsintar sa yayi akan titi.

“Zan yi wasu kalamai tare da masaniyar zasu fusatar da masoya na, makusanta da abokan arziki, akan su daina cin gyara na a turanci domin babu wanda na baiwa labarin nayi makaranta, akan tituna na tsinci wanda na iya a halin yanzu.”

Kamar yadda jaridar Dailypost ta ruwaito, jarumin ya bayyana cewar ya furta yaren turanci ne a fina-finai irinsu Gwaska returns, Bayan rai, da makanantan su don isar da sakon da fina-finan ke isawar ya zuwa wadanda basa fahimtar yaren Hausa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 18

“Tabbas na samu nasarori a wannan fagge, saboda haka masu cin gyara su kama gabansu domin yin abinda ya shafe su, kuma su barni na sarara. Bana bukatar gyaransu.

Kuje can ku ci gyaran wadanda suka yi nazarci yaren turanci domin ni kuwa ban iya furta shi a baka ba ballanta a rubuce.”

Link 1 DOWNLOAD VIDEO HERE

Link 2 DOWNLOAD VIDEO HERE

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.