Domin kallon cigaban shirin dadin kowa na satin da ya gabata.
ACIKIN WANNAN SATIN:-
Adama ta fara lallaba hannatu ta hanyar ba ta duk abin da take so, kama daga kana bin sha zuwa abin ci mai dadi, to sai dai kuma duk tana wannan ne don ta lallabata ta sha maganin tsayar da cikin dake jikinta.
A wani bangare kuma, Azumi ta fara nisa a harkar kayan maye, inda ta sami sabon salon boye wa Harisu ganyen da yake sayarwa a cikin maboyarta har da cikin matashin kai.
Ayuba maigadi na ci gaba da neman auren Hannatu, duk da yake bugu yake a cikin duhu, hakan bai hana shi kauce-kaucen rashin gaskiya ba a gudun da yake don kada su hadu da uban Hannatu wato Kamaye.
Bintu ta fara samun fahimtar juna a tsakaninta da I.B, al’amarin da ya faranta ran Yana.
A wani bangaren kuma adawa na kara tsananta tsakanin Malam Hassan da Malam Na’atala a lokaci guda kuma Kamaye na dab da shekawa lahira sakamakon hadarin da ya samu a wajen aikin gini.
Link DOWNLOAD VIDEO HERE
Vidmate: DOWNLOAD VIDEO HERE
Add Comment