Wasanni

Varane Ya Amince Da Komawa Manchester United

advertisement

Wasu rahotani daga kasar Ingila sun bayyana cewa dan wasa Raphael Varane ya amince da yarjejeniyar kwantiragin buga wa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wasa zuwa shekara ta 2026, amma ba a kai ga cimma yarjejeniya da Real Madrid a kan dan wasan bayan ba.

Har yanzu dai Manchester United ba su kai ga tayin Varane a hukumance a gun Real Madrid ba, amma suna bibiya ganin sun samu amincewar dan wasan, kuma kungiyar ta kasar Spain sun amince dan wasan na iya barin Santiago Bernabeu.

Ba a sa ran canza sheka, kuma Varane, wanda yake matukar girmama Real Madrid bai mika bukatar barin kungiyar ba, saboda ya gwamnace ya yi ta jira har sai an warware batun makomarsa.

Ganin cewa kwantiragin Varane, wanda ya shafe shekaru 10 a kungiyarsa Real Madrid zai kare a shekarar 2022, akwai bukatar Real Madrid ta dauki matakin sabantawa ko kuma ta yi hannun riga da shi.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dai tana ganin zata iya samun Varane akan kudi fam miliyan 45 sai dai Real Madrid ta ce dole sai United din ta biya sama da hakan wanda hakan ne yasa har yanzu ba’a cimma matsaya ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button