Uwargidan Gwamnan Bauchi Ta Dauki Nauyin Karatun Yara Sama Da 150 Dake Sansanin Gudun Hijira

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A kokarin gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Barista Mohammed Abdullahi Abubakar wajen bunkasa harkar ilmi, kamar yadda kowa ya sani a kasafin da aka fitar, ta warewa fannin ilmi kaso 20.

Haka kuma a ci gaba da habbaka fannin ilmin a jihar ta Bauchi, Uwargidan Gwamnan jihar Bauchi, Hadiza M.A Abubakar ta hannun kungiyarta ta NGO mai suna B-SWEEP ta samarwa yara ‘yan sansanin gudun hijira 150 da ma wasu yara marasa gata gurbin karo ilmi

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Yaba Wa Gwamna Mai Mala Kan Inganta…

1 of 661

A yayin jin ta bakin mai taimakawa Gwamnan Bauchi kan harkokin sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar ya bayyana cewa duba da irin wannan hobbasa da Gwamna M.A yake yi a fannin ilmi da sauran ayyukan ci gaba a jihar, akwai bukatar a sake zabar sa domin ci gaba da gudanar da ayyukan alkairan da yake shimfidawa a fadin jihar.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: