Babban taron mata na kasashen Arewacin Amurka da Afirka da na gabas ta tsakiya, watau SAMEAWS 2018 ta zabi Hajiya Hadiza Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin shugaba da ta yi fice.
An ba ta kyautar ne a yayin taron kungiyar ta 2018 da a ka yi a birnin Dubai.
Kungiyar SAMEAWS ta ce ta zabi uwargidan Gwamnan ne saboda gudumawar da ta ke bayar wa wurin inganta rayuwar mata da matasa a jihar Bauchi karkashin shirinta na (BSWEEP).
Haka kuma an bai wa Hajiya Hadiza takardar shaidar girmamawa daga Georaia a taron.
Mataimakin gwamna na musamman kan harkokin sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar ya ce daga karshe Uwargidan gwamnan ta gabatar da takarda a wurin taron mai taken inganta rayuwar mata da kananan yara mai dorewa a jihar Bauchi.