Usman Abdallah Ya Sake Sabon Kwantaragi Da Enyimba

1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba International dake garin Aba a jihar Abia ta sake karawa kociyan kungiyar Usman Abdallah sabon kwantaragi na shekara biyu domin ya ci gaba da zama a kungiyar.

Kungiyar ta Enyimba dai ta yanke shawarar karawa tsohon kociyan na Kano Pillars kwantaragi ne bayan da taga kungiyoyi a gasar firimiya ta kasa sun fara shirin tuntubarsa domin ya bar kungiyar yakoma wata kungiyar.

Felid Anyasi Agwu, shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafar ta Enyimba ya bayyana cewa sun yanke shawarar karawa kociyan sabon kwantaragi ne bayan da sukaga irin kokarin da kungiyar tayi a kakar wasan data gabata a wasannin gida dana mahiyar Afirka.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

Nasan Annabi Muhammadu Shine Mutumin da Yafi Kowa a Duniya…

1 of 54

“Duk da cewa labarin cewa mai koyarwa Abdallah zai sake sabuwar yarjejeniya ba wani babban labari bane amma ya kamata in sanar da duniya cewa mun yanke shawarar ci gaba da zamansa a kungiyar tare da wadanda suke taimaka masa.

Ya ci gaba da cewa “Mun san girman kungiyarmu kuma mun san irin wadanda ya kamata su kasance suna koyar da ‘yan wasanmu hakan yasa muka yanke shawarar ci gaba da zamansa domin ci gaba da zaman Enyimba babbar kungiya a Najeriya.

Mai koyarwa Usman Abdallah dai ya samu wanann damar ne ta ci gaba da zama a kungiyar bayan da yakai kungiyar wasan kusa dana karshe na gasar zakarun nahiyar Afirka sanann kuma kungiyar ta kammala kakar wasan data gabata a matsayi na hudu.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: