Sabuwar Jarumar nan a masanaantar Kannywood wacce ke fitowa a cikin shirin Film ɗin Labarina, Ummi Karama ta lashe gasar zama Gwarzuwar Jaruma ta shekarar 2022.
Jaridar Amintacciya ce ta shirya gasar tsakanin jarumai mata na Kannywood, inda bayan sanya Jaruman cikin gasar a ƙarshe mabiyan Jaridar Amintacciya suka zaɓi Ummi Karama, a matsayin Gwarzuwar Jaruma ta shekarar 2022.
Yadda Jaridar ta gudanar da zaben shine Jaridar ta fitar da cewa zatai zaben ne ta hanyar sanya hotunan waɗanda ake gasar dasu, duk wacce tafi samun wadanda sukai like da hoton ta ita ce zata yi nasara.
A cikin jarumai mata na Kannywood din, da jaridar ta wallafa hotunan su Ummi Karama ce wadda tafi samun waɗanda sukai like da hoton ta.
Jaridar ta Amintacciya ta fitar da Ummi Karama a matsayin Gwarzuwar Jarumar ta a 2022 inda ta bayyana cewa ba ita tai zaben ba mabiyanta ne.
A karshe wannan Jarida tana taya Gwarzuwar Jaruma Ummi Karama Murnar samun wannan Nasara daga Mabiyan ta.
Add Comment