Labarai

TURKASHI | Ɗan shekara 20 da ya yi garkuwa da mahaifinsa tare da karɓar kuɗin fansa har ₦2000,000

Yan sanda sun cafke wani matashi ɗan shekara 20, Abubakar Amodu wanda ya jagoranci garkuwa da mahaifinsa da karbar kuɗin fansa har naira miliyan biyu.

Amodu na cikin mutane 25 da aka cafke wanda jami’in hulda da jama’a na ƴan sandan Najeriya, CP Frank Mba ya sanar, kan laifuka daban-daban a Abuja.

Matashin ya shaida wa ƴan jarida cewa mahaifinsa na kiwon shanu, sannan ya kara da cewa ya karbi shanu 15.

Ya shaida yadda ya ƙula abokanta da muggan abokan da suka ba shi shawarar ya sace mahaifinsa saboda yana da arziki, zai kuma samu kuɗi ta hanyar.

Matashin ya ce ya samu naira 200,000 a cikin miliyan guda da suka karba.

Yanzu haka dai za a gurfanar da wannan matashi domin ya fuskanci shari’a.

✍️ BBC Hausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: