Muhawara

TURƘASHI | Uwa Ta Jefar Da Jaririnta A Kwandon Shara Saboda Ya Yi Kama Da Tsofaffi

Wata mahaifiya ta yi watsi da sabon haihuwarta a cikin kwandon shara saboda irin halittar da Allah ya yi masa.

Matar da ba a san ko wacece ba ta haifi da mai kama da dattijo kuma ta watsar da shi a kwandon shara da aka lullube a cikin bakar jakar roba, a inda wani dattijo yana wuce wa sai ya ji kukan karamin jaririn ya cece shi.

Bayan dattijon ya dauki yaron sai ya kai shi wurin tsohuwar matarsa domin kula da shi, bayan sati hudu yaron ya kamu da rashin lafiya kuma ya zama dole ne su dauke shi zuwa asibiti wanda yake da nisa sosai da kauyensu. Lokacin da suka isa asibitin, sai likitocin suka gaya wa tsofaffin ma’auratan cewa an haifi yaron ne da wani yanayi da ake kira ‘Pogeria’.

Wannan yanayin yana sa yara saurin tsufa kuma yana sanya fatar su yin yaushi, wanda ke sa su zama kamar tsofaffi. Tsoffin ma’auratan sun ce za su reni jaririn a matsayin nasu kuma su ba shi duk kaunar da yake bukata ko da kuwa sun tsufa wajen renon jariri.

Mahaifiyar yaron har yanzu ba ta zo don masa cewa nata ba ne, amma ana zargin cewa wata budurwa ce wacce ba ta san yadda za ta kula da yaron ba bayan da ta girgiza da irin kamanninsa.