Ƴar jaridar nan mai gabatar da shirin Alkiblah a gidan radiyo da talabijin na Liberty da ke jihar Kaduna, Ayshatu Adam Gimbiya ta yi wani kira mai kama da kashedi kan cewa za su rika tsayar da masu zuwa zance wajensu har dare domin hukunta matan mazajen da suka hana su ƙara aure.
Tun da farko Ayshatu Adam Gimbiya, ta bayyana wannan ra’ayin na ta ne a cikin salo irin na nishaɗi tare da zolaya a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwambar 2020.
“Hmm… Ba dai kun ki bari su auro mu ba. To wallahi mu ma ba za mu dinga bari su dawo gida da wuri ba.” In ji Ayshatu Adam Gimbiya
Wannan furuci na ƴar jaridar ya jawo cece-kuce, inda ya sha martanin nuna rashin goyon baya musamman daga matan aure, ya yin da a gefe guda kuma, wasu maza su ka nuna jin dadinsu ga kalaman na Aysha Gimbiya.
Add Comment