-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Tsoro Ne Ya Hana Ganduje Halartar Muhawarar BBC?


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya kauracewa muhawarar da BBC Hausa ta gudanar a Kano ranar Asabar.

Ganduje shi ne gwamna mai-ci a jihar ta Kano, wanda kuma ke son a zabe shi karo na biyu.

BBC Hausa dai ta gayyaci Gwamna Ganduje da ‘yan takara hudu domin tafka muhawara kan abubuwan da za su sanya a gaba idan suka lashe zaben gwamnan jihar.

Sauran ‘yan takarar da aka gayyata wadanda dukkansu sun halarci muhawarar su ne Abba Kabir Yusuf na PDP, Salihu Sagir Takai na PRP, Mustapha Getso na jam’iyyar NPM DA kuma Maimuna Muhammad ta UPP.

Dukkan ‘yan takarar sun amsa tambayoyi daga wurin BBC da kuma jama’ar da suka halarci muhawarar kan al’amura daban-daban da suka shafi rayuwar mazauna jihar.

Sai dai Gwamna Ganduje bai samu damar halartar muhawarar ba, wacce za ta ba shi damar wayar da kan masu kada kuri’a kan batutuwan da zai mayar da hankali idan ya sake cin zabe.

Gwamnan na jihar Kano bai bayyana dalilansa na kauracewa muhawarar da BBC Hausa ta shirya ba, ko da yake wasu na ganin hakan ba zai rasa nasaba da tambayoyin da ake so ya amsa game da batutuwa da dama ba.

Gwamna Ganduje dai ya shiga bakin ‘yan Najeriya a shekarar 2018 bayan wata jarida da ake wallafawa a intanet, Daily Nigerian, ta fito da wani bidiyo da ya nuna shi yana karbar abin da ake zargi cin hanci ne.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

A bidiyon, an nuna gwamnan na Kano yana karbar damman daloli yana sanya wa a aljihu.

Sai dai gwamnan ya sha musanta zargin.

Shi kansa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sha suka a wurin ‘yan kasar wadanda suka yi zargin cewa bai dauki mataki kan gwamnan ba suna masu cewa ba gaskiya ba ne ikirarin da yake yi na yaki da cin hanci da rashawa.

Buhari da GandujeHakkin mallakar hotoTWITTER/@DAWISU

Sai dai Shugaba Buhari ya ce bai san irin na’urar da aka yi amfani da ita wajen sarrafa bidiyon ba.

A cewarsa, “A ce kamar gwamnan Kano yana dariya yana karbar daloli abin mamaki ne.”

A ranar Alhamis lokacin da shugaban kasar ya je yakin neman zabe jihar Kano, ya daga hannun Gwamna Ganduje, matakin da wasu ke cewa amincewa ne da cin hanci.

Sai dai tun kafin zuwansa jihar, Shugaba Buhari ya ce ya kamata a bar kotu da majalisar dokokin jihar su yanke hukunci kan gwamnan.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: