Daga Anas Saminu Ja’en
Ko dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta i’shi ‘yan arewa ishara musamman wadanda suke cikin kunshin gwamnati suna gudun jama’arsu, Sun Yadda Cewar Bako Ya fi Dan Uwa. To kuna gani duk fadin kasar nan a arewacin Nijeriya kurum aka nuna murna da dawowar sa saboda kishin sa da suke yi kuma a nan yake da miliyoyin masoya manya da yara.
Sabanin sauran sassa kasar nan wadanda sunfi kowa morar wannan gwamnati ta Buhari da sauran abun da ya shafi harkar tattalin arzikin kasa, amman suka ki nuna farin cikin su da dawowar Buhari To Su Sani Cewar Cuta Ba Mutuwa Bace.
Ina masu hankalin Arewa dake cikin gwamnatin tarayya zuwa jihohi muddin idan har da gaske kuke son shugaban kasa Muhammad Buhari, sai ku dawo daga rakiyar su ku dawo gida ku rungumi mutananku ku nemi hadin kan sauran al’umma masu kishi a yi wani sabon tsari na ciyar da arewacin Nijeriya gaba tun kafin lokaci bai gama kurewa ba. mun san cewar duk lalacewar duniya ba a rasa na Allah Ta’ala idan kuma baku motsa dan kawo gyara a Arewa ba. To zamu yi muku kudin Goro mu ce kuna jin dadin abun dake faruwa.
Kar fa ku manta duk fadin Najeriya Arewace kurum bata da wani tsari nata na kanta ko a Fannin ilimi ko a fannin kasuwanci ko tsarin siyasa ko a fannin abun da ya shafi tattalin arziki ko a fannin abubuwan more rayuwa da sauran ababe da daman gaske.
Allah ya kara kare mana Shugaba Muhammadu Buhari. Allah ya kara masa hikima ya taya shi sauki nauyin dake wuyansa, amin.
Add Comment