Muhawara

Tsokaci Akan Mutane Masu Dogaro Da Wannan Kalmar Ta Buhari Komai Zai Sauki 2017

Assalamu Laikum Yan uwa musulmai yau muka shiga sabuwar shekara ta 2017 
Yau zanyi Tsokaci Akan yan uwana musulmai wanda sukai imani da buhari akan 2017 komai zai yi sauki 

Nasan Kunsan Wannan Hotan Waye A Jiki 
Wannan Shine shugaban kasar nageriya Wato General Muhammadu Buhari Maici A Yanzu 
Kuma Yayi Jawabi Akan 2017 Komai Zaiyi Sauki Sukuma Mutane Kowa Ya Dogara Da Wannan Shekarar Iya Jira Komai Yayi Sauki 
Da Kayima Mutum Abu Sai Kaji Iyakira bara 2017 Tayi Tunda Bahari Yace Komai Zaiyi Sauki 
TO WAYE BUHARI 
Kowa Yasan Buhari Mutum Ne Kamar Kowa Shima Ransa A Hannun Allah Yake Kuma Nasan Shikansa Buharin Insha Allahu Da Allah Ya Dogara  Shi Kawai Dai Iya Kan Mulki Ne Da Allah Subahanahu Wata Allah Ya Zabeshi Ta Sanadiyar Mutane  Da Suka Bada Kuri,unsu Sukaje Sukai Zabe Suka Dan gwalamasa Amma Da Allah Yayi bashi Zai Mulkemuba Da Koshine Yaci Ba Zai Hau Wannan karagarba 
Mutane Duk Sun manta Da Allah Sun Kama Buhari A Lokacin Da Muke Tsakiyar Tashin Hankali Kowa Ya Rude Sai Baba Buhari 2015 A Wannan Lokacin Bama Tunanin Wata Yunwa Ko tsadar Kaya 
Kawai Muga Mun Fita Daga Wannan Masifar Da Ta Addabemu Musamman Mu Arewaci 
Sai Allah Ya Kawo Wanda Ta Silarsa Wannan Bala,in Zamu Fita Daga Cikinsa Amma Kuma Dole Wannan Kau Da Bala,in Sai An Shiga Wata Masifar Ko Ince Wata Bala,i. 
Ankau Da Wancen Masifar Sai Aka Turomana Da Wata Domin A Gwada Imanin Mu Aga Suwaye Sukai Imani Da Allah Da Kuma Suwaye Suka manta Da Allah Suka Riki Buhari.
A Dan Wannan Lokacin Matsin Da Akashiga Sai Wasu Suka manta Da Masifar Baya Suna Zagin Buhari Da yake Sun riki gwamnti Ita Take basu Kudi Take basu Abinci To Da Sukaji babu Sai Suka Koma Zagi Da Kirawo masifar Da Ta Wuce Suna Dawo Da Ita Saboda Dama Su da Gwamnati Suke Dogara 
Shima Kansa Buharin Da Kuke Gani Ta Kansa Yake Yanzu Ana Cewa Kunfa Yakun Ta Mutuwa To Wlh Ko Second Daya ba Zai Karaba Indai Ajalinsa da Aka Rubutamasa Lokaci Yayi 
Shawarata Anan Yan Uwa Itace Indai Harkai Imani Da Wayannan Abubuwa Guda 6 To Kada Ka Taba Sama Kanka Damuwa A Kanwani 
1- Imani Da Allah 
2- Imani Da Mala,iku 
3- Imani Da Manzanni 
4- Imani Da Litattafai  Sune Irin Su QUR-ANI da INJILA da ZABURA da ATTAURA 
5- Imani Da Ranar Lahira 
6- Imani Da Kaddara   Ta ALKAIREE ce Ko Ta SHARRI 
Kunga Wayannan Abubuwa Guda Shida INdai Kayarda Dasu To Shine Kake Da Cikake Imani 
Dan Allah Mutane Mu Gyara rayuwarmu
Komai Zamuyi Mudinga Sawa Da Insha Allahu
Idan Kasamu Dama Ka Turawa Abokanka Na Shafin Sada Zumunta

Idan kanada Kuma Wata Shawara Da Zaka Bayar Kana Iya Nemanmu Ta Nan
08148337698

Happy New Year

Allah Kasadamu Da Alkaireen Dake Cikinta Ka Tsaremu Da Duk Sharrin Dake Cikinta

Rubutawa

Abubakar Rabiu