Labarai

Tsohon Shugaban Kasa, Jonathan Ya Ziyarci Jihar Bauchi Domin Kaddamar Da Ayyukan Da Gwamna Bala Ya Yi

Daga Lawal Mu’azu Bauchi
Tsohon shugaban kasar Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ziyarci jihar Bauchi don duba tare da bude wasu ayyuka karkashin gwamnatin Sanata Bala Muhammad.

Shugaba Jonathan wanda ya isa jihar Bauchin a safiyar yau ya samu tarba daga Gwamna Bala Muhammad, Mataimakinsa Sanata Baba Tela, Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Mohammed Sabiu Gwalabe, Shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Dakta Ladan Salihu, kwamishinoni, shugabannin kananan hukumomi, masu mukamai, Yan siyasa da kuma dumbin al’umar da suka yi wa filin tashi da saukar jirage na Sir Abubakar Tafawa Balewa tsinke.

Jonathan ya fara da ziyarar gaisuwa da neman tabarruki daga fadar me martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleiman Adamu inda sarkin ya yaba masa kan zuwa Bauchi da kuma kaunar da yake nuna mata.

Nan take Masarautar Bauchi ta nada Shugaba Jonathan mukamin “Jigon Bauchi na farko ”

Daga nan tsohon Shugaban Kasar ya zaga Birnin don duba ayyukan raya Kasa ciki har da sabon titin Sabon Kaura da aka sanya sunansa.

Jonathan ya yabawa Gwamna Bala Muhammad kan ayyukan raya Kasa da gwamnatinsa ke gudanarwa inda yace ko shakka babu Gwamna Bala zai cire kitse a wuta la’akari da kwazon sa tun lokacin da ya rike mukamin ministan Birnin Tarayya Abuja.

Ya yabawa Masarautar Bauchi da al’umar jiha kan tarba da kaunar da suke nuna masa inda yace yana da cikakken imanin Najeriya zata cigaba tare da shawo kan matsalolin da take fama da su.

Jonathan yace Gwamna Bala Muhammad hazikin gwamna ne me kishi kana ya jinjina masa kan biyayyar da yake nuna masa yayin da bayan ya bar mulki.

Lawal Muazu Bauchi
Me tallafawa Gwamna Bala Muhammad kan kafafen yada labarai na zamani
21/4/6

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: