Tsohon Kwamishina Da Magoya Baya 10,000 Sun Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC A Jigawa

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tsohon kwamishinan sharia karkashin tsohuwar gwamnatin Alhaji Sule Lamido a jihar Jigawa Barista Yakubu Abdullahi Ruba tareda magoya baya samada dubu goma sun sanarda sauya shekarsu daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Ruba wadda ya jogoranci wannan gungun magoya baya ya bayyana ficewarsu daga jam’iyyar a jiya a babban birnin jihar dake Dutse.

Tsohon kwamishinan wadda ya share shekaru hudu ya jagorantar fannin sharia a gwamnatin tsohon gwamna Alhaji Sule Lamido ya ce, sun fice ne sakamakon danne hakkin ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP da shugabanninta ke yi wadda a cewarsa suma basu tsallake ba.

Ya kuma bayyana cewa, ya dauki wannan mataki ne bisa wadansu dalilai gamida tattaunawa ta musamman da dumbin magoya bayansa dake fadin jihar ta Jigawa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

“Na bar jam’iyyar PDP bisa wasu dalilaina da kuma wasu kudurorina da gudummawar da nake son baiwa al’umma wadda in har ina jam’iyyar ba zai yiwu ba” in ji Ruba.

Haka kuma ya bayyana cewa, duk da kasancewarsa cikin jam’iyyar ta PDP tun lokacin kafuwarta a shekarar 1999, amma yanzu lokaci ya yi da zai bada gudummawarsa ga shugaba Buhari, gwamna Badaru da kuma yankinsa domin cigaban kasa.

Ruba ya kuma umarci dukkan magoya bayansa dake jihar baki daya da su amsa wannan kira nasa tareda tattara duk komatsansu domin sauya sheka zuwa jam’iyyar ta APC.

Daga karshe ya kuma godewa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP bisa dama da ta bashi a baya har ya rike matsayin kwamishina na tsawon shekaru hudu.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: