Siyasa

Tsohon Gwamnan Bauchi Da Magoya Bayansa Sun Koma Jam’iyyar GPN

Tsohon Gwamnan Bauchi Da Magoya Bayansa Sun Koma Jam’iyyar GPN

Tsohon gwamnan jahar Bauchi Malam Isa Yuguda ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar GPN (Green Party of Nigeria) tare da magoya bayan shi da dama.

 

Sun hada da tsohon sakataren PDP, Alhaji Umaru Dahiru, tsohon minista Alhaji Habibu Aliyu, da kuma tsoffin kwamishinonin da masu yi masa yakin neman zabe.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan Alhaji Salisu Ahmad Barau shi ya bada wannan sanarwa, da cewar gwamnan ya yanke hukuncin ne a wani taro da ya halarta a garin Jos a ranar Asabar da ta gabata.