Daga S-bin Abdallah Sokoto
Yanzu haka shahararren tsohon daraktan shirya finafinan Hausa a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Ashiru Nagoma ya fara samun sauki.
Jama’a idan zaku tuna watanni biyu da suka wuce an tafka muhawara akan shi saboda irin halin da ya shiga na rashin lafiyar kwakwalwa(Tabin-Hankali) cewa jaruman masana’antar Fim ta Kano basu kyauta ba barin shi a wannan hali.
To sai dai Gidauniyar @Creativehelpingneddyfoundation ta dauki nauyin kai shi Asibiti tareda bashi kulawa ta musamman, kuma cikin ikon Allah an fara samun nasara sosai.
Ubangiji Allah ya kara bashi lafiya da sauran masara lafiya.