Tsoffin Janar Din Sojojin Nijeriya Sama Da 50 Sun Goyi Bayan Buhari Ya Zarce

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tsofin janar a rundunar soji ta sama, kasa, da ruwa sun bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari domin sake zama shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

A yau Litinin ne tsofin Janar din sojojin suka shaida wa duniya goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari a zaben da za a yi ranar 16 ga watan Fabarairu da mu ke ciki.

Talla

Tsofin janara-janar din sun hada da ma su mukamin manjo janar 13, Air Vice Marshal (AVM) 8, Rear Admiral 2, birgediya janar 12, Air Commodore 9, Commodore 8 da kuma wasu tsofin shugabannin rundunar soji 17.

Tsohon gwamnan jihar Legas a mulki soji, Birgeiya janar Buba Marwa (mai ritaya) ne ya jagoranci tsofin janar-janar din yayin da su ke bayyana goyon bayan su ga takarar shugaba Buhari a yau.

Daga cikin tawagar tsofin janar-janar din akwai Navy Capt Caleb Olubolade, tsohon ministan harkokin ‘yan sanda lokacin mulkin Jonathan da kuma tsohon shugaban rundunar sojojin ruwa ta kasa, Admiral Jubril Ayinla.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Goyon bayan tsofin sojojin na zuwa ne bayan shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya ce manyan tsofin janar na soji da ke kasar nan na kulle-kullen kawo karshen gwamnatin shugaba Buhari ta kowacce hanya.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin gabatar da tutar takara ga gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, a filin taro na Malam Aminu Kano da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Ya bayyana cewar tspfin janar din sojin na son ganin bayan gwamnatin shugaba Buhari ne saboda irin aiyukan da Buhari ke yi ga jama’ar Najeriya ya saba wa bukatun su.

Oshiomhole ya kara da cewar sha’awar shugaba Buhari na son kyautata wa talaka ne babban dalilin da yasa tun a farko tsofin janar na sojin ke murde ma sa zabe tun a baya.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: