-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

`Tsoffi Da Suka Haura Shekara 70 Su Hakura Da Takara Su Bar Wa Yara Masu Jini A Jika- Abdussalami


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tsohon Shugaban kasa a mulkin soja Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa duk wani dan siyasa da yasan yayi shekaru 70 ya kamata ya hakura haka yabarwa matasa kuma, 

Abdussalami yayi wannan bayani ne a Kaduna, a wani shagube da ake zaton ya yiwa shugaba Muhammadu Buhari ne , wanda aminansa Obasanjoda IBB suka juyawa baya a bana.

Sai dai kuma, dan takarar da ake zaton suna marawa baya, wato, Atiku Abubakar, shima ya haura 70 din.

Tsohon Shugaban soja Abdulsalami Abubakar ne ya bada wannan shawara a Arewa House dake jihar Kaduna a yayin kaddamar da wani littafimai suna “Yakowa: A dream differed”.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 656

- Advertisement -

Ya kara da cewa idan kuma suna tunanin suna da karfin da zasu iyayin shugabancin to su sanya kishi a cikin zukatansu dan samawa kasar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Tsohon gwamnan jihar yace “yan siyasar dake tunanin suna da karfin mulkar kasar nan to su sanya kishi ta haka ne zasu samu damar saisaita kasar”.

“Ina shawartarku da kuyi kamfe a bisa abubuwan da suka kamata,Y’an siyasa da jam’iyunsu su rike wani abu wanda zai samarwa da kasar kwanciyar hankalinmu kuma zamuci gaba da basu shawara akan abinda ya kamata har zuwa lokacin da kasar zata zama mai inganci. “

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: