Labarai

Tsawon Shekaru 27 Kenan Sheik Bashir Baiyi Magana Da Kowa Ba Saboda Karama (Hoto)

Sama da shekaru 25 da suka gabata kenan, shahararren malami dan kasar Sudan Sheik Bashir Muhammad Bashir ya dakatar da yin magana, wanda hakan ya sa jama’a suka fara yi masa lakabi da Malamin da ba ya yin Magana.
Kafar yada labarai ta Al’arabiya ta baiyana cewa, shi dai malam Bashir ya kasance ya na yin tadi da duk wanda yake so ta hanyar rubutawa a takarda ko allo. Haka kuma shehin ya halarci bita da dama tare da kasancewa a tattaunawa da gidajen talabijin amma duk da haka sai dai ya mayar da amsar tambayar da aka yi masa ta hanyar rubutawa a takarda.
A wata tambaya da aka yi masa a hirarsa da gidan talabijin, Bashir ya bayyana cewa bai taba yin nadama ba kasancewarsa ya janye bakinsa daga yin magana, domin yin hakan ita ce mafita.
Ya kara da cewa alkalamin da yake amfani da shi, kawai ya na kwantar da hankalin abokanan mu’amullarsa. Inda ya cigaba da cewa ya fi samun nutsuwa a duk lokacin da ya kame bakinsa.
Shehin ya bayyana hikimarsa ta yin shiru ta hanyar rubuta cewa “a daidai lokacin da aka rufe baki zai kasance karshen Magana kenan ”. Yace halin da ya jefa kansa, sirri ne a tsakaninsa da Ubangijin da ya hallice shi.
Sheik Bashir an haife shi a shekarar 1956, ya kasance ya na da mabiya da dama da suke karkashinsa a kasar Sudan, kuma ya kammala digirinsa na farko a jami’ar Sorbonne, wanda daga nan ne ya yi tattaki zuwa kasar Faransa inda ya sami digiri na biyu kan fannin kimiyar tattalin arziki.
Bayan ya dawo gida ne ya kuma maida hankali wajen gudanar da bincike da karatun Al’kur’ani, inda a shekarar 1990 ya dakatar da yin magana da kowane mahaluki.
Ga hoton yanda Sheik Bashi yake magana da mutane a kan wani karamin farin Allo.