Labarai

Tsaro: Hukumar NCC Za Ta Datse Layukan Sadarwa A Zamfara

A wata takarda da hukumar sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta aikewa kamfanon kafafen sadarwa na Nigeria, ta umarce su da su datse layukan sadarwar jihar Zamfara na tsawon kwanaki biyu, a cewarsu hakan yana da alaka da dakile barazanar hare-haren ‘yan bindiga a jihar da makobtanta.

Takardar wacce babban sakataren hukumar, Farfesa Umar Dambatta ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa kamfanonin su gaggauta yin hakan, don taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da aikinsu cikin nasara. Daga yau 3 ga Satumba umarnin zai fara aiki.

A kasance tare da mu don samun cikakkun labarai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: