- Advertisement -
A wani bangare na magance matsalar tamowa, gwamnatin Najeriya na tunanin bullo da shirin ciyar da kai, da ta kira ‘Operation Feed Yourself’ a turance.
A cewar mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, shirin na da zimmar karfafa wa manoman zamani da na kauyuka samar da abinci wadatacce ga al’umma.
Mr Osinbajo ya yi jawabinsa a wani taro kan ”ingantaccen tsarin abinci” da aka yi a Abuja, wanda ya samu halartar mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed, da wasu gwamnonin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.
An yi hasashen cewa za a fuskanci karanci da kuma tsadar abinci a Najeriya a 2022.
Amma a cewar mataimakin shugaban kasar, lokaci bai kure ba da za a yi amfani da shirin na ‘Operation Feed Yourself’ don hada hannu wurin ceto al’umma daga fadawa cikin yunwa.