Tsageru Neja-Delta Sun sha Alwashin Hana hako mai
Murna za ta koma ciki idan aka yi sake a Najeriya don kuwa Tsagerun Neja-Delta za su koma fasa bututun mai kamar yadda su ka fada.
A yanzu haka dai Najeriya na hako sama da ganga Miliyan 2 na danyen mai a kowace rana.
Ana ma sa rai hakan ya karu kamar yadda Ministan kasafin kudi Udo Udoma ya bayyana kwanan nan a wani taro da aka yi a Legas.
Wasu tsageru da ke Yankin Neja-Delta sun aikawa Dattijon Yankin Edwin Clark takarda cewa za su koma fasa bututun man kasar har sai ta kai ba a iya hako komai a Najeriya.
Wannan dai zai zama babbar matsala ga tattalin kasar idan aka yi sake.
Alkaluman kasar kamar yadda muka samu daga Fadar Shugaban kasa sun tabbatar da cewa tattalin arzikin kasar ya kama hanyar mikewa sarai.
Add Comment