Labarai

Trump zai tattauna da Buhari ta waya

A ranar Litinin ne ake sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da misalin karfe 3.45 na yamma ta wayar tarho.
Haka kuma bayan tattaunawa da Buhari, Mista Trump zai kira shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma da misalin karfe 4.10 na yamma.
Wannan dai shi ne karon farko da Shugaba Trump zai tattauna da wasu shugabannin Afirka tun bayan shan rantsuwar kama aiki da ya yi a watan Janairu. 
Ba a san dai takamaiman batutuwan da Mista Trump zai tattauna da shugabannin na Afirka ba.
Sai dai tun a lokacin da Mista Trump ke yakin neman zabensa bai nuna wata sha’awa ta mu’amala da Afirka ba, saboda yadda ba ya sako batun nahiyar a al’amuransa.
Hakan ya sanya fargaba kwarai a zuciyar shugabannin nahiyar bayan da Mista Trump ya lashe zabe, saboda rashin tabbas game da yadda dangantakarsu za ta ci gaba da gudana.
Najeriya ce kasar da tafi ko wace yawan al’umma a nahiyar Afirka, kuma akwai dubun-dubatar ‘yan kasar da ke ci-rani a Amurka.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.