Labarai

Trump ya dora wa Obama alhakin zanga-zangar kin ‘yan jam’iyyar Republikan

Shugaba Trump (a hagu) ya Obama (a dama) shi ne ya kitsa zanga-zangar kin ‘yan jam’iyyara Republikan da ake yi
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya yi amannar cewar Barack Obama ne ya kitsa jerin zanga-zangar kin ‘yan majalisar dokokin kasar na jam’iyyar Republikan da kuma fitar da wasu bayanan tsaron kasar. 
Trump ya shaida gidan talabijin na Fox News cewar, “ina tunanin shugaba Obama ne ya kitsa lamarin saboda tabbas mutanensa ne suka hada abin. Na kuma yi tunanin cewar siyasa ce kawai.”
Mista Trump bai bayar da wata hujjar ikirarinsa ba, kuma magabacinsa a fadar White House, Barack Obama, bai yi tsokaci kan batun ba tukunna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: