Trump ba ya so Palasdinawa su samu kasar kansu
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da shirin kasarsa na shekara da shekaru wanda ya amince cewa kafa kasa biyu tsakanin Isra’ila da Palasdinu shi ne kawai hanyar magance rikicin da ke tsakaninsu.
A wani taron manema labarai da ya yi tare da Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, Mr Trump ya yi alkawarin samar da abin da ya kira wata “babbar” yarjejeniyar zaman lafiya, sai dai ya ce dole ne duk bangarorin su sassauto daga matsayin da suke kai.
Rabon da Isra’ila da Palasdinawa su yi wata tartibiyar tattaunawa kan zaman lafiya tun shekarar 2014.
Mr Trump ya bukaci Mr Netanyahu ya dakatar da gine-ginen da yake yi na gidajen Yahudawa a yankunan Palasdinawa “zuwa wani dan lokaci”.
Isra’la dai ta bayar da umarnin gina dubban gidaje a yammacin Kogin Jordan da kuma Gabashin birnin Qudus tun lokacin da Mr Trump ya sha rantsuwar kama aiki a watan jiya.
Ofishin jakadanci
Gwamnatin Isra’ila tana fatan inganta dangantaka da Amurka bayan ta kwashe shekara takwas tana ja-in-ja da gwamnatin Barack Obama.
A wajen taron manema labaran na ranar Laraba, babu daya daga cikin shugabannin da ya fito fili ya goyi bayan samar da kasar Palasdinu, wanda ke daya daga cikin manyan muradun da Amurka ta dade a kansa.
Za a samu kasashe masu cin gashin kansu?
Amurka da sauran kasashen duniya sun dade da amincewa kan samar da kasashe masu cin gashin kansu ga Isra’ila da Palasdinu.
Hakan zai bayar da damar samar da mazauni na dindindin ga Palasdinawa, kamar yadda yarjejeniyar da aka kulla gabanin shekarar 1967 ta amince, inda za su zauna a Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza da Gabashin birnin Qudus cikin lumana tare da Isra’ila a bangare guda.
Majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashen Larabawa da ta Tarayyar Turai da Rasha, da kuma Amurka, in ban da yanzu, sun sha nanata wannan matsayi.
Add Comment