Labarai Politics

Tinubu zai zo Kano domin kaddamar da wasu aiyuka – Ganduje

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano domin kaddamar da wasu aiyuka – Ganduje

 

Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ana sa ran zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu zai zo jihar kano domin bude wasu aiyuka da gwamnatinsa gudanar a nan kano.

 

” A yayin da muka cigaba da bude wasu daga cikin aiyukan raya kasa da gwamnatinmu ta yi a kwarya birnin kano da kewaye, Muna sa rana Zaɓaɓɓen Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano domin kaddamar da sabuwar gadar da muka Samar a kofar mata zuwa Ibrahim Taiwo Road”.

 

Kadaura ta rawaito, Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwar ta jihar kano na wannan makon a gidan gwamnatin jihar kano.

 

Ganduje yace ya bude aiyuka Masu tarin yawa Kuma zai cigaba da bude aiyukan don raya kasa da gwamnatinsa ta gudanar.

 

Ganduje dai ya na bude aiyukan da ya gudanar ne a wani bangare na bankwana ga al’ummar jihar kano sakamakon karewar wa’adin gwamnatin sa a ranar 29 ga watan mayu.