-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Taron Motsa Jam`iyyar APC A Jahar Katsina


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

GANGAMIN MOTSA JAM’IYYAR APC A JAHAR KATSINA

Daga Mainasara Nasarawa Funtua

A jiya Asabar ne Kungiyar matasan jahar Katsina masu kishin Jahar Katsina suka shirya Gaggarumin Gangamin baje kolin Aiyukan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Da Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari.

An Gudanar da Gangamin ne a cikin Garin Katsina, inda aka fara daga Hedikwatar Ofishin jami’iyyar APC, Daga nan aka bi ta kofar Durbi zuwa Filin Wasa na Muhammadu Dikko.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

- Advertisement -

Taron ya had’a shahararun Mawakan Hausa, irin su Rarara, Alan waka, Baban Chinedu, Isyaku Foris da Sauran su, da ‘yan Wasan Hausa irin su Ali Nuhu, Rukayya Dawayya, Jamila Nagudu da sauran su, haka nan kuma Akwai ‘Yan social Media, masu tallata Aiyukan jam’iyyar APC, Gamayyar Matasan ta sanya Gasar Rawa ta Wakar Baba Buhari Dodar, Wanda Daraktan Kamfen na Mawakan Shugaban kasa Dauda kahutu Rarara ya rera.

An gudanar da gasar ne tsakanin matasa daga jahohin arewacin kasar nan, anba na daya kyautar Mota, na biyu Keke Napep, Sai na uku Mashin Roba Roba, Haka Nan akwai rukunin kungiyoyi guda Goma, An basu dubu Hamsin Hamsin.

Jinjina ga masoyin Shugaban kasa Muhammad Buhari Da Gwamna Aminu Bello Masari, Engr Muntari Sagir Malumfashi.

Shugaban Kamfanin Gine-Gine na Muntasrab, Injiniya Muntari Sagir Malumfashi, shine ya dauki nauyin Gudanar da Gangamin da bada kyaututtaka.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: