Labarai

TARON GANGAMIN BUHARI A KANO YA GAMU DA CIKAS

 

Daga Salisu Yahaya Hotoro

Taron Gangami da mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen sadarwa Mal. Shaaban Ibrahim Sharada ya shiryawa jihogin Arewa maso yammacin Nigeria ( Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa, Sokoto, Kebbi da Zamfara) domin yin murnar dawowar shugaban kasa daga jiyya ya gamu da cikas bayan da mutane suka ki fitowa taron.

Tunda farko dai masu shirya wannan taro sun ikirarin zasu Tara mutane Miliyan 3 a babban filin wasa na Sani Abacha dake nan Kano.

Masu kididdiga sunce mutanen da suka halacci wajen wannan taron daga jihohi 7 basu wuce 500 ba.

Ku bayyana ra’ayinku akan abubuwan da kuke ganin sun kawowa wannan taro tarnaki.

Allah ya bawa Buhari ingantacciyar lafiya.