Tarihin Shaikh Nurayn Muhammad Siddiq

0 99

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Zakariyya Shu’ab Adam

An haifi shaikh Nurayn a garin Furjab da ke kusa da garin Bara a yankin Kurdufan na ƙasar Sudan, a shekarar 1982. Ya karanci Qur’ani a gun mallamai da dama a garinsu, kamar shaikh Al-makkiy. Allah ya azurta shi da haddace Qur’ani a shekarar 1996 a hannun shaikh Abdurrahim Rashid. Bayan ya kammala hadda, sakamakon kyawawan ɗabi’unsa da ƙanƙan da kai, an zaɓe shi a matsayin shugaban ɗalibai a babbar tsangayar da ke Furjab.

Shaikh Nurayn ya wakilci ƙasar Sudan a musabaƙar Qur’ani da aka yi a ƙasashe da yawa. A shekarar 2005, ya zo na biyu a musabaƙar duniya a ƙasar Saudiyya. A 2006 ma ya sake yin na biyu a musabaƙar duniya ta ƙasar Libya. Hakazalika ya wakilci Sudan a musabaƙar Malaysia da Dubai.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 10

Shaikh Nurayn ya jagoranci sallah a masallatai da yawa a ciki da wajen Sudan. Daga cikinsu akwai babban masallacin Khartoum da masallacin An-nur. Allah ya azurta shi da murya mai daɗi da ke ratsa zuciya. Duk da cewa yana yin riwayoyi mabambanta, sai dai ya fi shahara da yin karatu da riwayar Hafs Ad-duriy ‘an Abi Amr. Shaikh na daga ne cikin mallaman da ke yawo gari-gari domin da’awah da karantarwa.

A shekaran jiya Juma’a, shaikh Nurayn tare da wasu mallamai kuma alarammomi guda uku, sun gamu da hatsarin mota yayin da suke dawowa daga da’awah daga garin Wādī Ḥalfā da ke jahar arewa ta Sudan. Sun yi hatsarin ne a wani wuri da ke da nisan kilomita 18 daga garin Umm Durmān. Duniyar musulunci ta yi alhinin rashin wannan bijimin alaramma. Tun daga shekaran jiyan, ba bu abin da kake gani a kafafen sada zumunta ban da hotuna da bidiyon karatuttukan Shaikh Nurayn. Babu shakka ya samu yabo daga al’umma.

Allah ya gafarta wa Shaikh Nurayn

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: