Tarihin Sabon Babban Hafsan Sojin Kasan Nijeriya Manjo Janar Farouk Yahaya

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ko Kun San Cewa Janar Yahaya Farouk Dan Asalin Jihar Sokoto Ne?

…ku karanta takaitaccen tarihinsa

Daga Comr Abba Sani Pantami

An haifi Manjo Janar Farouk Yahaya a garin Sifawa na karamar hukumar Bodinga da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya a shekarar 1966.

Ya shiga aikin soja a 1985 a matsayin dan aji na 37 inda ya kammala karatun soji a ranar 22 ga watan Satumba na 1990.

Ya samu karin girma a rundunar soji kamar haka:

Laftana – ranar 27 ga Satumba 1990

Kyaftin – ranar 27 ga watan Satumba 1994

Manjo – ranar 27 ga watan Satumba 1998.

Laftanar Kanar – ranar 27 ga watan Satumba 2003.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 10

Kanar – ranar 27 ga watan Satumba 2008

Birgediya Janar – ranar 27 ga watan Satumba 2013

Manjo Janar – ranar 27 ga watan Satumba 2017.

Sabon babban hafsan sojin kasan na Najeriya ya yi karatun digirinsa na farko a fannin Tarihi sannan ya yi digiri na biyu wato Masters a kan harkokin siyasar kasashen duniya da difilomasiyya.

Ya rike mukamai daban-daban ciki har da mataimakin sakataren rundunar soji da kuma sakataren na rundunar soji a hedikwatar sojin kasa.

Mukamin da ya rike na karshe kafin naɗin nasa shi na jagorantar yaƙi da Boko Haram karkashin rundunar Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya.

Ya taɓa riƙe muƙamin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko wato General Officer Commanding (GOC) 1 Division.

Kafin nadinsa a mukamin General Officer Commanding 1 Division, Manjo Janar Yahaya ya jagoranci runduna ta 4 da ke hedikwatar rundunar sojin Najeriya.

Kazalika ya rike mukamin Kwamandan rundunar Lafiya Dole da ke Maiduguri, a jihar Borno.

A shekarar 2019, Manjo Janar Farouk Yahaya ya jagoranci rundunar Operation CLEAN SWEEP wadda ta fatattaki ‘yan bindigar da ke dajin Kuduru a Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: