Tarihin Mawaki Umar MB A Takaice

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Assalamu Alaikum A yau bakonmu na wannan satin muna tare da Mawakin Umar MB wanda yai wannan wakar fim din gwaska return wato ( Zancen Soyayya), ga yadda hirar tamu ta kasance.

ArewaBlog, Da Farko Dai Zamu Danso Muji Tarihinka Da Kuma Cikakaken Sunanka.

Talla

Umar MB, Da farko dai sunana umar musa wanda aka fi sani da umar mb an haife a garin rigasa dake garin kaduna nayi makaranta ta a kaduna kuma ina ci gaba da karatuna a nan din.

ArewaBlog, Wace Gwagwarmaya Kasha?

Umar MB, Gwagwarmaya lallai ansha ta wadda ba zata misaltu ba daga koyan aiki da sauransu.

Talla

ArewaBlog, Wane Kulu Bale Ka Fuskanta?

Umar MB, Ai babu wata sana a ko kuma al’amari na ci gaba da zakayi da babu kalu bale a cikin sa na fuskaci kalu bale amma gaskiya dukkan lamura ana samun nasara.

ArewaBlog, Yaushe Ka Fara Waka?

Umar MB, Na fara waka tun ina makaranta ne, kuma gaskiya na fara wakar makaranta ne.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 9

ArewaBlog, Wace Wakarce Bakandamiyarka?

Umar MB, Wakar da mutane suka fi so itace bakandamiya ta.

ArewaBlog, Wace Shawara Zaka Bawa Yan Uwa Masu Tasowa?

Umar MB, Shawara kuma da zan ba masu sana a irin tawa shine su dage da aikin su indai da rai da rabo wata rana za a samu nasara da yardar allah kawai a tsaftace zuciya kiyayya hassada da sauran su basu kai mutum ga tudun dafawa.

Wannan itace hirarmu da mawaki Umar MB ta shafin sada zumunci na Instagram.

Kuma kuna iya neman wannan mawakin ta shafin kawai kusa ” Realumarmb ”

Gamusu bukatar suma a sanya nasu kuna iya tura mana sako ta Email dinmu ([email protected])

Allah kasa Mudace

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: