Addini

TAMBAYA: Wace Sallar Nafila ce tafi daraja cikin Nafilolin da Annabi yayi – Imam M Bello Mai-Iyali

TAMBAYA: Wace Sallar Nafila ce tafi daraja cikin Nafilolin da Annabi yayi.

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Sallar nafila aiki ne na ibada da bawa yake yi don nuna biyayya ga Allah da neman kusanci agareshi zuwa gareshi.

Nafila nada mahimmanci ga bawa don tana cike giben da akesamu a sallar falilla. Kuma tana kusantar da bawa zuwa ga mahaliccinsa. Sallah ita ce mafificeyar ibada.

Sallar nafila tafi daraja a cikin dakin mutum, matukar ba wadda ake yi a wani guri na musamman ne ba. Annabin rahama (SAW) yayi kuma ya koyar da nafilfili da yawa a gurare daban- daban.

Bababu wani nassi karara da ke nuna sallar nafilar da tafi girman daraja a kan sauran nafilfili baki daya, kowace nafila tana da falala mai girma, Sallar nafilar dare tafi na rana, kuma sallar nafila a cikin daki yafi a masallaci, kuma sallar idi tafi dukk wata nafila a ranar idin, sallar wutiri tafi sauran nafilfilin dare, sallar rokon ruwa da na kisfewan rana da wata sun fi daraja a lokacin da ake bukatar su, sallar asham tafi girman daraja a lokacin ta kuma a cikin jam’i, haka dai za ka ga wata tafi wata daraja a wani yanayi.

Lura da girman darajan sallar nafila a musulunce, malaman Fiqihu sun kasa sallolin nafila zuwa gida uku:

a) Nau’in sallar nafila mafi girman daraja sune ake kira da SUNNA MAI KARFI KO SUNNA WAJIBA. Waddanan sallolin nafila sun fi sauran girman daraja a musulunci. Sallolin Sunna Mai Karfi ko Sunna Wajiba guda goma ne:

1) Sallar Wutiri
2) Sallar Idi karama
3) Sallar Idi Babba
4) Sallar Kisfewar Rana
5) Sallar Kisfewar Wata
6) Sallar Rokon Ruwa
7) Sallar Raka’atanul Fajri ( raka’a biyu kafin Sallar asuba)
8) Sallah Raka’a biyu na Dawafi
9) Salla Raka’a biyu na harama da aikin hajji
10) San sujadar Karatun al-kur’ani agurin Imamu Malik.

Dukkan sallonlin nan Annabi ya dawwama a kan su har karshen rayuwar sa, yayi umurni da yinsu. Sabo da Girman darajar su, wasu malaman ma suna ganin waddanan sallolin wajibi ne. An tsarosu ne bias darajarsu ta daya tafi ta biyu kamar yadda ta uku ta fi ta hudu har zuwa karshe.

b) Nau’in sallar nafila mafi girman daraja a mataki na biyu su ne ake kira da FADA’IL. Waddanan sallolin nafila suna da girman daraja amma basu kai goman farko ba:

1) Raka’a biyu bayan alwala
2) Raka’a biyu na gai suwar masallaci (tahiyatu masjid)
3) Sallar walaha (salatut duhah)
4) Tsayuwar dare (tahajjud)
5) Sallar asham (tarawihi)
6) Sallar shafa’i
7) Sallolin nafila kafin da bayan sallar farilla (sunan al-rawatib)

c) Nau’in sallar nafila mafi girman daraja a mataki na uku su ne ake kira da NAFILFILI. Waddanan sallolin nafila suna da girman daraja amma basu kai mataikai biyu da suka gabata ba:

1) Sallar nafilar da batada munasaba ko lokaci, nafilar da bawa yake yi a dukk lokacin da ya samu dama cikin lokutan da ya hallata a yi nafila

2) Nafilar da matafiyi ke yi a lokacin da zai fara tafiyar sa da kuma
lokacin dawowo daga tafiyar sa (raka’a biyu)
3) Nafilar shiga da fita daga gida (raka’a biyu)
4) Sallar istikhara (raka’a biyu)
5) Sallar bukata (salatul hajah) raka’a biyu
6) Sallar tasbihi (salatut tasbih) raka’a hudu
7) Nafila raka’a biyu a tsakanin kiran salla da tada iqamah
8) Sallar nafila (raka’a biyu) a lokacin da mutum zai tuba zuwa ga
Allah (salatut taubah)
9) Sallar nafila (raka’a biyu) a lokacin da mutum zai yi addu’a
10) Sallar nafila (raka’a biyu) a lokacin da sojoji zasu shiga yaki

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.