TAMBAYA: Menene hukuncin Mutumin da yake cewa a addu’a ” Allah kayi mini Kaza saboda Annabin Ka Muhammad (SAW).”?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Addu’a da Annabi (SAW), (wato, rokon wani abu, a ce don Annabi kai tsaye) ba shari’a ba ne, musulmi zai roki Allah da sunayensa kyawawa, ko tsarkakan siffofinsa, ko da imaninsa da shi Allan, ko da kyawawan aikinsa, ko da sonsa da yakeyiwa Allan, ko da addu’ar wani bawan Allah da yayi masa.
Amma babu laifi mutum yace: Allah kayi mini Kaza saboda da son da nikewa Annabin Ka Muhammad (SAW), domin son Annabi ibada ce da za’a iya yin tawassuli da ita, kuma zai iya cewa: dan daraja da alfarman Annabin ka Muhammad (SAW).
Baya halatta bawa ya roki (tawassuli) Allah da Annabi, waliyi ko salihan bayin Allah, kamar yadda bai halatta a roki Allah da JAHIN ko HAQQIN wani ba, kuma wajibi ne mutum yabar hakan idan yana yi.
‘Yan-uwa mu roki Allah da abinda ya shar’anta, wato, da sunayensa, sifoffinsa, imani da shi, Kalmar shahadah, ayyukan kwarai, ko addu’o’in bayin Allah. Wannan ita ce fatawar mafi yawan Malaman musulunci.
Allah ka tsarema imamninmu da mutuncinmu. Amin.
Source Premiumtimes Hausa
Add Comment