TAMBAYA AKAN GASHI A CIKIN ALKUR’ANI MAI GIRMA. 

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Sheik Malam Aminu Daurawa

TUN JIYA AKE BUGO MINI WAYA AKAN WAI WANI YA YI MAFARKI YA GA ANNABI MUHAMMAD SAW, WAI YACE MASA A BUƊE ALKURNANI CIKIN SURATUL BAƘARA, ZA A GA GASHI SAI A JIƘA A SHA YANA MAGANIN CORONA VIRUS.

MANZON ALLAH SAW YACE :DUK WANDA YA YI MINI ƘARYA YA TANADI MASAUKINSA A CIKIN WUTA. BUKHARI DA MUSLIM

 

WANNAN MAFARKI DA WANNAN MAGANA BA GASKIYA BACE SABODA DALILI GUDA GOMA:

NA ƊAYA, MAFARKI DA ANNABI SAW GASKIYA NE, AMMA SAI KA GAN SHI YADDA YAKE A KAMANNINSA DA MAGANGANU SA DA HALAYANSA, WANNAN KUWA BAI YI KAMA DA YADDA ANNABI SAW YAKE ISAR DA SAKO BA, GASHI DA ALKUR’ANI.

NA BIYU, ME YA HAƊA DA ALKUR’ANI MAI GIRMA DA KUMA GASHI?

NA UKU, GASHIN NA WAYE, MUTUM KO DABBA? KUMA NA INA NE GASHIN?

NA HUƊU, DUK WANI GASHI IDAN BA NA ANNABI SAW BA, TO ZAI ZAMA KO ƘAZANTA KO NAJASA

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 18

NA BIYAR, ME YASA BA’A YI AMFANI DA ALKUR’ANIN BA SAI GASHIN KAWAI?

NA SHIDA, ME YASA SAI A AFRIKA KAWAI AKE SAMUN WAƊANNAN SHIRMAN

NA BAKWAI, WAYE YA BUƊE ALKUR’ANIN KUMA YAGA GASHIN?

NA TAKWAS, INA WANDA YAGA MAFARKIN YAKE?

NA TARA, AN GWADA AKAN MAI CIWAN YA WARKE? KO YA WARKE BA ZAI ZAMA GASKIYA BA, DOMIN ZAI IYA ZAMA JARRABAWA.

NA GOMA, ANYA BA SHEƊANU BANE DA BOKAYE, DA MASU SIHRI SUKE SON HALAKA MUTANE? DOMIN AYI WASA DA ALKUR’ANI MAI GIRMA DOMIN WATA MUSIFAR TA ƘARA SAUKA, KAMAR YADDA YA FARU A LOKACIN IBOLA DA GISHIRI?

ALLAH YA TSARE MANA IMANI DA AKIDA YA YAYE MANA DUKKAN BALA’I.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: