Takaitaccen Bayanin Binciken Da Nayi Game Da Aikin Man Fetir Din Jihar Bauchi

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Ni (Abdulhadi Isah Ibrahim) a matsayina na dan jihar Bauchi ina godewa Allah, da ya azurta jihar mu ta Bauchi da arzikin man Fetir, sannan ina kara yaba wa Shugaba Buhari da wannan kokari, ina rokon Allah ya tsare jihar mu daga irin matsaloli da jihohin Niger Delta suka fada saboda arzikin man Fetir da Allah ya zuba a yankin, ina fatan Allah ya kame hannun matasan mu daga fasa Bututun man Fetir ko kuma wani abinda yake da amfani a wannan fanni.

Abinda nake so na rubuta game da wannan man Fetir na jihar Bauchi shine, hakika nayi bincike kwarai dai dai gwarwado akan wannan aiki, daga cikin abinda na tattara na bayanai wasu sun sani wasu basu Sani ba, shine, babu wani Shugaban kasa a Nigeria da ya taba yunkurin ganin Arewacin Nigeria ya mallaki rijiyoyin man Fetir sai Shugaban kasa Buhari.

Talla

A lokacin da yake mulkin soja ya gayyato Manyan masu binciken man daga kasashen waje suzo su duba ko akwai ko babu, suka yi masa karya cewa babu, idan ma akwai dan kadan ne Wanda bazai kai a biya kudin aikin tonon ba ma balle a sayar a kasashen duniya, wannan kuma al-ada ce ta kasashen Turawa idan suka gane yankin ku akwai man Fetir ko a kasar ku baza su yarda su fada muku ba, domin haka wani injiniyan Man Fetir ya sanar dani, a Shekarun 1960s zuwa 1970s haka suka yi irin wannan karyar wa Saudi Arebia da Qatar, Bahrai, Kuwait da sauran su.

Bayan sun sanar da Shugaba Buhari a wancan zamani (1985) a lokacin shi kan sa Buhari bai yarda ba, sai ya sake nemo wasu daga kasar Rasha sun zo sun fara aiki sai Babangida ya kifar da gwamnatin sa a 1985 a watan August ranar 31, tun daga lokacin aka binne maganar samar da man Arewacin Nigeria, suka kori Turawan kuma suka sace kudin da Buhari ya ajiye don aikin man Fetir din Arewa, shima Buhari aka kama shi aka daure a gidan Yari na tsawon Shekaru 3, kafin daga baya aka fitar dashi.

Haka aka shafe Shekaru 33 babu Wani Shugaba da ya sake dago batun, sai a 2016 Shugaba Buhari ya sake maganar kuma ya ware biliyoyin kudi domin aiki, Alhamdulillah yanzu an samu rijiyoyin man Fetir masu yawa wanda aka qiyasta za’a iya kaiwan Shekaru 80 ko fiye ana diban danyen man Fetir daga cikin su.

Talla
Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Daga cikin tattaunawar da nayi da wani, injiya masani akan ilimin man Fetir ya sanar dani cewa, ana iya duba wuri a samu babu man Fetir amma wata ran idan aka dawo aka duba ana iya samu, (Saboda kyauta ce ta Allah sai lokacin da ya ga daman zuba shi a wuri), kuma hakan ta faru lokacin da Buhari yake mulkin soja, lokacin da yaso ya tonon man Fetir din Arewa, amma gaskiya an boye masa gaskiyan abubuwa da dama akai, a wancan lokacin, kuma wata matsalar itace sai suka kawar dashi daga mulkin, bai samu dama balle ya gano bayan nan da suka boye masa a wancan lokacin (1985).

Wani abin haushi a lokacin da Obasanjo ya hau mulki a 1999 wasu masu kishin Arewa sun je sun same shi akan batun man Fetir din Arewa, sai ya nuna musu bazai yi ba, ba wannan bane a gaban sa, daga bisani a 2002 ya aika aka toshe hanyoyi da ramukan da Buhari ya fara tonon a 1984 aka toshe su 2002, shiyasa da Buhari ya dawo zai sake tonon sai aikin yayi wahala kuma kudin yayi yawa, da ace Obasanjo bai toshe ba da tun bara an samu wannan nasara, amma hakan tasa sai yanzu nasaran ya samu.

Babban abin Mamaki kuma abin tambaya shine, me yasa Buhari ya dage sai lallai ya tono man Arewa? kana jin babu ne a jihohin Yarbawa ne? amsa itace tabbas akwai, jihohin Inyamurai ma akwai, amma me yasa bai je ya tone na can ba? zaka iya amsa tambayar da kan ka, yanzu haka jihar Gombe ce ya bata muhimmancin man Fetir din bayan jihar Bauchi, sai jihar Borno da Taraba, sai Benue da Sokoto da Zamfara, duk bayanai suna nuna cewa akwai man Fetir a wadannan jihohin kuma duk Buhari ya tsara sai ya tone su an fara amfani da man Fetir din Arewa cikin yardan Allah.

Zan tsaya anan, a rubutu na gaba zaku ji wasu abubuwa da za kuyi mamakin game da wannan yanki na Arewa akan batun man Fetir, Buhari zai kawo karshen gorin da kudu suke mana cewa, “Yan Arewa cima zaune sai dai a kai musu kudin man Fetir, basu da arziki babu karatu”, wadannan nasarorin ne su Obasanjo da Jonathan da Femi Fani Kayode da ire iren su suke jin zafi a zuciyar su, suke kara tsanan Buhari da neman ganin sun wargaza duk tanadin da Buhari yayi wa Nigeria dama Arewa.

Mutumin nan (Buhari) yana nan yana aiki kullum, don mu samu rayuwa mai kyau nan gaba, amma kai kana nan kana zagin sa a Facebook ko Majalisar unguwar ku, Saboda baka san me ake ciki ba, mayaudara sun yaudare ka kan ka ya rufe sai bakin magana da nuna gazawar Buhari, harshen ka bazai iya furta alkhairan sa ba, hannun ka bazai iya rubuta nasarorin da yayi ba, saboda baka san kan ka ba balle kasan me ya dace da kai.
Allah ya sauwaka.
By……..
Abdulhadi Isah Ibrahim.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: