Real Madrid na ci gaba da karfafa kungiyar wajen shigar da matasan ‘yan kwallo, domin tunkarar kakar wasanni da za a fara a cikin watan Agustan nan.
Tuni Madrid din a kokarin da take na ganin ta taka rawar gani a fafatawar da za a fara, ta sayar da ‘yan wasanta masu zaman benci kan kudi Yuro miliyan 110.
Real din ta sayar da Alvaro Morata da Danilo sannan ta bai wa Bayern Munich aron James Rodriguez domin ya buga mata tamaula shekara biyu, daga nan ta sayi dan wasan idan ya yi mata.
Chelsea ce ta sayi Morata kan kudi Yuro miliyan 80, wanda ya sa Real ta ci ribar Yuro miliyan 50 dan kwallon da ta dauka a Juventus kan Yuro miliyan 30.
Ita kuwa Manchester City ta sayi Danilo kan Yuro miliyan 30 kuma kudin da Madrid ta dauko dan wasan daga Porto.
Bayern Munich kuwa ta biya Madrid kudin daukar Rodriquez da zai buga mata wasanni aro, idan kuma ta ce za ta saye shi bayan shekara biyu, za ta biya Madrid Yuro miliyan 50.
Daga karshe Real ta sayarwa da Lyon matashin dan wasanta Mariano Diaz kan Yuro miliyan 10.
Real ta ci ribar sayar da ‘yan zaman benci.
BBCHausa
Add Comment