Tabbas Kwankwaso Ya Kawo Cigaban Gine -Gine A Jihar Kano -Ganduje

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tabbas Kwankwaso ya kawo ci gaban gine – gine a jihar Kano – Ganduje

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa tsohuwar gwamnatin jihar sa karkashin jagorancin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso

Talla

Ganduje ya yi wannan furuci ne a yayin amsa tambayoyin ‘yan jarida a karshe makon da ya gabata dangane da takaddama kan batun zaben kananan hukumomi na jihar, da kwantan bashi da ya yiwa jihar katutu da kuma wasu ababe da suka shafi jihar.

A yayin amsa tambayoyin ‘yan jarida, Ganduje ya bayyana cewa ko shakka babu tsohuwar gwamnatin Kwankwaso ta kawo muhimman ci gaba da kuma habaka ta fuskar gine-gine.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 325

Gwamnan ya yiwa wannan fashin baki yayin amsa tambayoyi dangane da gine-ginen gidaje da tsohuwar gwamnatin jihar ta kaddamar a wasu sassa dake iyaka da birninjihar.

Sai dai Ganduje ya ce gwamnatin sa ba za ta iya ci gaba da gudanar da wannan aiki ba sakamakon tsadar kayan aiki da kuma sauyin yanayi na tattalin arziki a kasar nan baki daya.

A karshen makon da ya gabata jaridar ta Daily Trust ta kuma ruwaito cewa, gwamnan ya bayyana ainihin bashin dake kan jihar ta Kano, inda ya bayyana adadin kudi na N300b da tsohuwar gwamnatin Kwankwaso ta bari.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ganduje ya kalubalanci duk wani mai takaddama kan batun sakamakon zaben kananan hukumomi na jihar akan ya shiga kotu idan yana da hujjoji

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: