Kannywood

Ta Rabawa Marayu Kayan Sallah – Maryam Booth

Jaruma Maryam Booth tayi rabon kayan sallah ga marayu kananun yara maza da mata a Nasarawa dake kano. jarumar ta raba shaddoji da yadika masu din ki da ado na zamani. awajen rabon ne wakiliyar mu Maryam Hotoro ta sami sukunin zantawa da jarumar kamar haka:

 

Maryam kin rabawa marayu kayan sawa, kuma da alamu wadan nan yara marayune, wanne hange ki kayi wanda yasa ki ka rabawa marayu kayan sallah amadadin ki ba masu iyaye?

 

Wannan tambaya tana da saukin amsawa. domin amsarta yana cikin tambayarki. duk yaron yake da iyaye to tabbas yana da tabbacin samin kayan sallah, amma maraya bashi da tabbas. dan haka naga gwara in ba marayu zaifi kyautuwa.

 

Me za kice da yan uwanki jarumai akan irin wannan abin alkairi da ki ki gudanar a yau?

 

Abinda zance shine, su ma Allah ya basu ikon gudanar da wannan abin alkairi. duk da yake da yawan jarumai maza da mata suna irin wannan abin alkairin, nima da wasu nayi koyi. irinsu A Zango, Sani Danja, Ali Nuhu.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.