Fitacciyar jarumar Kannywood Jamila Nagudu ta gode wa ‘yan uwa da abokan arziki wadanda suka duba ta da kuma yi mata addu’a a lokacin da ta kwanta rashin lafiya.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, jarumar ta ce “Allah mun gode maka; Allah ka kara mana lafiya. Marasa lafiya na gida da asibiti birni da kauye Allah ka ba su lafiya.
Ta kuma mika godiya ga ‘yan uwa da masoyanta da suka je duba ta a asibiti.
Sannan ta kara da cewa “Nagode sosai. Allah ya bar zumunci”.
A makon da ya gabata ne jarumar ta wallafa wani hoto da ke nunata a kwance tana jinya.
Sai dai kawo yanzu ba ta bayyana irin cutar da ke damunta ba.
Jarumai irin su Ali Nuhu da Aisha Tsamiya na cikin jaruman da suka yi addu’ar samun lafiya ga jarumar.
A wani sako da ya wallafa a shafinta na Instagram, Ali Nuhu ya ce “Allah ya ba ki lafiya daughter [‘yata – kamar yadda ya saba kiranta]”.
A nata bangaren, Aisha Tsamiya ma ta yi wa jarumar addu’a, inda ta ce “Ubangiji Allah ya ba ki lafiya sis [‘yar uwa].
Jamila Nagudu ta yi fice wajen taka rawa daban-daban.
Add Comment