Ta Ina `Yan ISIS Suke Samun Taimako Makamai Da Kudi?

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Datti Assalafiy

Shekaran jiya Lahadi 6-1-2019 Sojojin ‘kasar Syria (Syrian Arab Army SAA) sun gano wani katoton dakin ajiyar makaman yaki har da makamai masu linzami a garuruwan Talbiseh da Taldou a arewacin birnin Homs na ‘kasar Syria

Talla

Daga cikin makaman da sojojin suka gano sun hada da:
-RPG-18 anti-tank rocket-propelled grenades
-RPG-22 anti-tank rocket-propelled grenades
-RPO-A thermobaric rocket launcher
-RShG-2 thermobaric rocket launcher
-Machine guns
-AK47s
-AAs
-Ammunition of different calibers
-Satellite Communication Systems

Wannan shine karo na biyu da sojojin ‘kasar Syria suka gano babban gurin ajiyar makamai a birnin Homs, kwanaki hudu da suka gabata wato ranar juma’ah 4-1-2019 a binciken da sojojin sukeyi suka gano muggan makamai wanda ‘yan ta’adda suka boye ciki har da wani makami da yake kakkabo makamai masu linzami wato “Anti-tank guided Missiles (ATGMs) kuma makamin kirar ‘kasar Amurka ne, da wasu muggan tarin makamai masu hatsari

Kasar Syria tana fama da matsalar kungiyoyi ‘yan tawaye masu neman ‘yanci irinsu kungiyar Hay’at Tahrir al-Sham (HTS) wacce reshe ce daga tsohowur kungiyar Al-Qa’idah, sannan sai kungiyoyin ta’addanci irinsu ISIS, kuma ya tabbata Amurka ita ke taimakon ‘yan ta’addan da kuma ‘yan tawaye, yayin da ‘Kasar Rasha (Russia) da Iran suke taimakon sojin ‘kasar Syria ana ta gwabza wannan yaki dubbannin rayukan musulmi yana ta salwanta

Kunga jama’ar musulmi Kasar Russia da Kasar Amurka sun hada rikici a gabas ta tsakiya, Rasha ta taimaki sojojin gwamnati, Amurka kuma ta taimaki ‘yan ta’adda da ‘yan tawaye ayi ta kashe musulmi, wannan rikicin na Syria da yadda Amurka ta kafa kungiyar ISIS ta shugabantar da tsoffin jami’anta na CIA irinsu Jihadi John da Abubakar Albaghdadi masifar bai kare a can ba, yau har ‘kasarmu Nigeria abin ya shafa

‘Yan uwa musulmi ina so mu dan tuna baya, kafin shekarar 1979 babu wata kungiya ta Musulmi da take rike da makami don tabbatar da shari’ar musulunci a dole, amma bayan tsohuwar tarayyar Soviet (Russia a yanzu) ta mamaye Afghanistan sai gwamnatin Amurka da kawayenta na kasashen Larabawa suka baiwa Malamai izni su shellanta “Jihadi” a Afghanistan

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Gwamnatin Amurka sai ta dauki nauyin horarwa da dabarun yaki (Training and logistics) a wadanda zasuyi aikin jihadin, su kuma kasashen Larabawa kawayen Amurka sai suka dauki nauyin biyan duk wani abu da mayaka (Mujahideens) zasu bukata wato (financing), sai aka sa General Haqq na Pakistan yayi declaring Jihadi akan ‘kasar Russia, aka gayyaci dukkan Musulmai daga ko ina a duniya zuwa Pakistan, da aka tara musulmai sai a ka rabasu runduna uku, rundita ta farko Larabawa karkashin jogarancin wani Malamin Eygyt (na manta sunansa) wanda su Usama bin Laden suke karkashinsa, musulmi masu bin tafarkin ‘yan shi’ah aka waresu zasu kaddamar da jihadi akan Russia karkashin jagorancin Gulbuddin Hekmatayar, musulmin Afghanistan kuma karkashin Professor Rabbani

Haka suka hadu suka yaki tsohuwar tarayyar Soviet (Russia) aka gwabza yaki sosai, da aka gama cin nasarar korar Soviet daga Afghanistan, har sai da aka gayyaci su Usama Bin Ladan zuwa Washington DC don a karramasu, har tsohon shugaban ‘kasar Amurka Mr. Ronald Wilson Reagan (ya rasu a 2004) yayi kalmomin yabo ga su Usama bin Laden yace a kansu “they are the moral equivalent of America’s founding fathers”, wato su Usama wasu babban jigo ne na Amurka

Amma bayan anci nasaran korar Russia daga Afghanistan, sai wadannan Kwamandoji na Mujahidai suka karantar da fahimtar Sayyid Qutub a zukatan Mujahidan, aka gurbata musu tunani, cewa ayi amfani da karfin makami don tabbatar da shari’a a doron kasa, wanda wannan fahimtar bata samu karbuwa ba a gurin manyan Malaman Islama na duniya masu fatawa a wancan lokaci

To dai daga haka sai kowanne daga cikin kwamandojojin musulmi da suka kori Russia daga Afghanistan ya ware gefe da mutanensa, Professor Rabbani suka hada kai da Sheikh Umar wajen assasa kungiyar Taliban, su Usama bin Laden suka assasa kungiyar Alqa’idah, shi kuma Sheikh Adallah na Egypt ya assasa kungiyar ‘yan uwa musulmi “Muslim Brotherhood” (Ikhwan)

Jama’a wannan shine mafarin hanyar da Amurka tabi tayi sanadin samar da kungiyoyin ta’addanci masu alakanta kansu da musulunci a wannan karnin, kuma idan kun lura Amurka ta fara horar da ‘yan ta’addan tare da basu makamai.

Wannan hotunan makamai da kuke gani akwai videon a gurina, screenshort na daura muku.

Allah dai Ya sauwake mana, sannan Ya karemu daga dukkan sharri na kungiyoyin ta’addanci da masu daukar nauyinsu Amin

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: