Barcelona ta fara kakar La Liga ta Spaniya ta bana 2017/18 da kafar dama, bayan da ta ci wasa uku a jere karkashin Ernesto Valverde.
Ba wannan karon ne kungiyar ta fara cin wasa uku a farkon fara gasar ta La Liga ba, illa wannan karo ta banbanta da sauran.
Tun lokacin da aka fara gasar a 1928/29, sai a wannan karon ne Barcelona ta ci kwallo tara, yayin da guda daya kacal ta shiga ragarta.
A bana ta fara da cin Betis 2-0 a gida ta kuma yi nasara a kan Alaves sannan ta casa Espnayol 5-0 a Nou Camp.
A lokacin Luis Enrigue, kungiyar ta ci wasa uku a jere da fara La Liga a kakar 2013/14, inda ta ci kwallo tara amma kuma aka zura mata biyu a raga.
Bbchausa.com
Add Comment