Ta Dawo Kannywood Da Kafar Dama – Rahama Sadau

0 826

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tun bayan da aka kori Rahma Sadau daga kungiyar masana’antar fina finan hausa, sai ta koma yin fina finan Nollywood (fina Finan Kudancin Nageria).

Bayan jarumar tagane ta aikata laifi, ta bayar da hakuri ga kungiyar Moppan dama al’ummar Nageria gaba daya.
Kungiyar Moppan sanar da cewa ta dawo da jaruma Rahma Sadau kungiyar Kannywood, ma’ana yanzu daraktoci suna da yanchi da damar sa Rahma Sadau acikin fina finansu, ba tareda wata matsala ba.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 344

Za’a iya cewa, Rahma Sadau ta dawo kungiyar kannywood da kafar dama. domin fim din ta maisuna RARIYA yana daga jerin fina finan da za’a fitar amatsayin barka da sallah. wannan yasa Rahma Sadau yin murna da farin cikin dawo da ita da akayi masana’antar kannywood.
A wani bangaren kuma, wasu jarumai mata ba’a son ransu aka dawo da Rahma Sadau ba. sabida suna zaton zata iya hana su rawar gaban hantsi awajen wasu daraktocin kamar Ali Nuhu da Aminu Saira.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: