Get New DJ Mixes
Wasanni

Ta dauki dan wasa na biyar a bana – Man City

Mendy shi ne na biyar da ya koma City a bana

Manchester City ta kammala sayen mai tsaron baya na Monaco, Benjamin Mendy kan kudi fan miliyan 52 kuma na biyar da ta dauka a bana.

Dan wasan mai shekara 23, wanda ya koma Monaco daga Marseille a bara ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar.

 

Mendy shi ne dan kwallo na biyar da City ta dauka a bana, wanda ta kashe fan miliyan 200 wajen sayo ‘yan wasan.

City ta sayi Kyle Walker kan fan miliyan 45 da mai wasan tsakiya Bernardo Silva kan fan miliyan 43 da mai tsaron raga Ederson Moraes kan fan miliyan 35 da kuma Danilo kan fan miliyan 26.5.

Haka kuma kungiyar ta Ettihad ta sayar da Aleksandar Kolarov ga Roma kan kudi fan miliyan 4.5.

Man City ta kashe fan miliyan 201…

Kawo yanzu Manchester City ta kashe fan miliyan £201.5 kan sabbin ‘yan wasa a bana

  • Kyle Walker (Tottenham) – £45m
  • Bernardo Silva (Monaco) – £43m
  • Ederson Moraes (Benfica) – £35m
  • Danilo (Real Madrid) – £26.5m
  • Benjamin Mendy (Monaco) – £52m

 

Bbchausa

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.