Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya fadi zaben dan takarar Sanata a Kudu maso yammacin jihar.
Mr Ajimobi, wanda shi ne gwamna mai ci na jam’iyar APC ya samu kuri’a 92,218
Wanda ya lashe zaben shi ne Ademola Balogun na PDP da kuri’a 105,716.
Gwamna Ajimobi shi ne surukin gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda dansa Idris Ajimobi ya auri Fatima Ganduje.