Wasanni

Super Eagles Ta Koma Mataki Na 36 A Duniya

Tawagar kwallon kafar Nijeriya Super Eagles ta dan rage matsayi a sabon jadawalin FIFA na kasashen da suka fi iya buga wasa a duniya kuma Super Eagles, wacce ke matsayi na 34 a duniya a jadawalin FIFA na watan Satumba, ta rage maki 14 inda ta koma na 36 a duniya.

Koma-bayan na Eagles ya samo asali ne sakamakon rashin nasara da ta yi a gida a farkon wannan wata a wasan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta doke ta da 1-0 a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta 2022.

Duk da kokarin huce haushin su wajen doke CAR da ci 2-0 a Kamaru bai hana tawagar ta Gernot Rohr da rikitowa zuwa kasa ba, kuma Nijeriya wadda ke rike da kanbin gasar Afirka har guda uku ta ci gaba da rike matsayin ta na biyar a Nahiyar, inda Senegal har yanzu ke matsayi na daya a nahiyar kuma ta 20 a duniya, sai Tunisia ke biye ma ta a matsayi na biyu, amma ta koma ta 27 a duniya.

A halin da ake ciki, Belgium ta ci gaba da kasancewa ta daya a duniya duk da cewa ta yi rashin nasara a wasanni biyu a gasar UEFA Nations League, sai Brazil ce ta biyu, yayin da Faransa ke gaban Ingila zuwa matsayi na uku. Italiya ita ma ta kara zuwa matsayi na hudu, yayin Ingila din ke na biyar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.